Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama ya halarci bikin fara aikin da na'urar, inda ya ce, a cikin 'yan shekarun da suka gabata, tattalin arziki na bunkasa cikin sauri a Ghana, gashi kuma ana kara fama da karancin wutar lantarki.
Yace kafa tashar samar da wutar lantarki da karfin ruwa ta Bui zai sassauta wannan mawuyacin hali yadda ya kamata, tare da biyan bukatun masana'antu da na jama'a a wannan fanni.
Cikin jawabinsa, jakadan Sin a Ghana, Gong Jianzhong ya waiwayo babban sakamakon da aka samu da zumuncin da aka sada cikin shekaru 53 da suka gabata, bayan kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Ghana, inda yake ganin cewa, kafa tashar Bui ya sake bayyana dankon zumunci dake tsakanin kasashen biyu.
A shekarar 2008, bisa taimakon gwamnatin kasar Sin, aka fara aikin kafa tashar Bui a hukumance. Ya zuwa karshen shekarar nan kuma, dukkan tashoshi uku masu karfi 400MW za su fara aiki.(Fatima)