in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Cote d'Ivoire na kokarin samar da isasshen wutar lantarki a kasar
2014-05-16 14:15:08 cri

Ministan man fetur da makamashin kasar Cote d'Ivoire, Adama Toungara ya bayyana a ranar Alhamis a birnin Abidjan niyyar kasar Cote d'Ivoire ta samar da isasshen wutar lantarki.

Kasar Cote d'Ivoire na da burin kara samar da wutar lantarki domin cimma karfin megawatt dubu dari hudu a shekarar 2020, da zummar samar da isasshen wutar lantarki a kasar, in ji mista Toungara a yayin bikin dube dandalin kasa da kasa kan wutar lantarki.

A cewar ministan, manufar wannan dandali ita ce ta karfafa kwarewar kwararru da manajojin Afrika a bangaren samar da hanyoyin wutar lantarki na fasaha, ta yadda za'a kaddamar da wani tsarin da zai ingiza kasashen Afrika ga samun cigaba.

Wutar lantarki, wani muhimmin abu ne ga cigaban tattalin arziki da cigaban al'ummar wata kasa, in ji mista Toungara.

A nasa bangare, babban darekta janar na kamfanin wutar lantarkin kasar Cote d'Ivoire (CIE), Dominique Kakou, an aiwatar da dukkan hanyoyi domin rage karancin wutar lantarki a nahayar Afrika.

Kwararru da manajojin kasa da kasa fiye da 200 suka harlarci wannan dandalin kasa da kasa kan wutar lantarki tare da mai da hankali kan bullo da hanyoyi da dabarun da suka dace wajen bunkasa bangaren wutar lantarki a nahiyar Afrika. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China