An cimma wata yarjejeniyar zuba jari ta gamayyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika ECOWAS domin samar da kudade ga kasashe 3 wato Gambiya, Sierra Leone da Mali a bangaren samar da wutar lantarki bisa jimillar dalar Amurka miliyan 107.94 a ranar Litinin a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire.
An sanya hannu kan wannan yarjejeniya a gabanin taron kwamitin ministocin ECOWAS karo na 71 dake cikin tsarin gaggauta samar da makamashin wutar lantarki.
Kasashen uku za su samu wadannan kudade, inda kasar Gambiya za ta samu dalar Amurka miliyan 31.8, kasar Mali dalar Amurka miliyan 54.34, ita kuma kasar Sierra Leone za ta samu dalar Amurka miliyan 21.8.
Shirin na musamman da za'a aiwatar tare da tallafin kudin kungiyar ECOWAS, za'a yi shi bisa matakin taimakon kai tsaye ga wadannan kasashe uku inda ayyukan samar da wutar lantarki suke kasa ga bukatun jama'a, kuma yawan hanyoyin samun bunkasuwar tattalin arzikin sun kasance kalilan a manyan biranen wadannan kasashe uku da suka hada da Banjul, Bamako da kuma Freetown. (Maman Ada)