Mahukunta a kasar Afirka ta Kudu, sun ce, kasar na fuskantar karancin wutar lantarki da ba a saba gani ba, matakin da ya jefa birnin Johannesburg, cibiyar tattalin arzikin kasar cikin duhu.
Yanzu haka dai an fara gudanar da wani tsari na rarraba wutar lantarkin, tare da dauke ta a lokuta daban daban. A wani mataki na hana daukewa wani sashen kasar wutar gaba daya. Wannan ne dai karon farko tun bayan shekarar 2008, da kasar ta fuskanci wannan gagarumar matsala.
A ta bakin kakakin ministan ma'aikatar dake lura da kadarorin hukuma Mayihlome Tshwete, da ma dai Afirka ta Kudun na fuskantar matsalar wutar lantarki a baya bayan nan, sai dai a wannan karo, karancin ruwa a madatsan ruwan dake samar da lantarki, da karancin ingantaccen ma'adanin kwal, tare da raguwar wutar da kasar ke samu daga Zimbabwe, ya janyo ta'azzarar wannan matsala.
Duk dai da tasirin wannan matsala, wadda ta wajabtawa daukacin masu amfani da wutar rage kaso 20 bisa dari, na wutar da suke amfani da ita, a hannu guda, mahukuntan kasar sun alkawarta shawo kan wannan matsala nan da 'dan lokaci. (Saminu)