in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan kasar Sin ya gana da shugabar majalisar dokokin Afrika ta kudu
2015-04-07 21:03:25 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da shugabar majalisar dokokin kasar Afrika ta kudu Madam Baleka Mbete a nan birnin Beijing a yammacin yau Talata 7 ga wata.

Yayin ganawar nasu, Mr Li ya darajanta ci gaban da kasashen biyu suka samu waje raya dangantakar dake tsakaninsu, kuma ya nanata cewa, Sin na dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin bangarorin biyu, Sin na fatan kara yin mu'ammala tsakanin gwamnatoci, majalisu da jama'arsu tare da tabbatar da tsarin hadin gwiwa tsakaninsu, sannan kuma da sa ran cimma nasarar gudanar da taron ministoci na dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da Afrika a sabon zagaye, kuma da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar tsakanin kasashen biyu har tsakanin Sin da nahiyar Afrika zuwa wani sabon matsayi.

A nata bangare kuma, Madam Baleka Mbete ta nuna godiya sosai kan goyon bayan da Sin take bayar ta fuskar raya Afrika cikin dogon lokaci, da kuma taimakon da Sin ta baiwa Afrika wajen yaki da cutar Ebola, yana fatan kara habaka hadin gwiwa da kasar Sin da zurfafa mu'ammala ta fuskar al'adu da sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar tsakaninsu. Ban da haka kuma, yana maraba sosai ga kamfanoni da masu yawon shakatawa na kasar Sin da su kara zuba jari da kai ziyara a Afrika ta kudu. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China