in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin inganta sabbin sana'o'i
2015-03-23 09:37:36 cri

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya jaddada muhimmancin daukar matakan duk da suka wajaba, domin inganta sabbin sana'o'i, matakin da a cewarsa zai tallafa matuka wajen cimma burin da aka sanya gaba, na daidaita ci gaba, da fadada kirkire-kirkire, tare da samar da karin guraben ayyukan yi.

Mr. Li ya bayyana hakan ne yayin wata ziyarar aiki da ya kai sassan ma'aikatun dake kula da harkokin cinikayya da masana'antun kasar Sin, inda ya ce, ma'aikatun na da nauyin tabbatar da wadannan nasarori, musamman a wannan gaba da ake aiwatar da gyare-gyare ga tsarin bunkasa tattalin arzikin kasar. Kaza lika ya bayyana ma'aikatar cinikayyar da masana'antu, a matsayin ginshikin samar da jagoranci ga sauran sassan dake kasa, tare da hada ayyukan gudanarwa da na sanya ido.

Ya ce, kasar Sin na bukatar bunkasa sana'o'i, da samar da sabbin hanyoyin ci gaba, domin tabbatar da dorewar matsakaici, zuwa babban ci gaban da ake fata.

Daga nan sai ya jaddada aniyar mahukuntan kasar game da yaki da kayayyaki na jabu, da satar fasaha, da ma burin samun amincewar jama'a don gane da ingancin kayayyaki kirar kasar Sin. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China