A yayin taron, an ce, rahoton aikin gwamnatin da aka zartas a taron majalisar wakilan jama'ar kasar Sin shi ne alkawarin da gwamnati ta yi wa jama'ar kasa, don haka ya kamata hukumomin da abin ya shafa su gudanar da ayyukansu yadda ya kamata bisa kamar yadda aka tsara a cikin rahoton.
Kaza lika, a yayin taron, an gabatar da manyan fannoni guda 12 na aikin gwamnatia, yayin da manyan ayyuka guda 62 suka shafi wasu hukumomi, haka kuma, an jaddada cewa, ya kamata gwamnati ta cika alkawarin da ta yi wa jama'a. (Maryam)