A cikin jawabinsa, Li Keqiang ya bayyana cewa, yanzu an fara yin kwaskwarima kan fasahohin zamani a wani sabon zagaye, inda kasashe da dama sun gabatar da manufofinsu kan inganta fasahohin zamani. Gwamnatin kasar Sin ta yi la'akari da halin da ake ciki a kasarta da matakin bunkasuwarta a halin yanzu, ta gabatar da wani shiri mai taken 'Aikin kera kayayyaki a kasar Sin a shekarar 2025' a matsayin hanyar raya sha'anin kera kaya na kasar Sin a shekaru 10 masu zuwa. Kana za a fadada hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Jamus a fannonin yanar gizo, sadarwa da dai sauransu.
A nata bangare, shugabar gwamnatin Jamus Merkel ta nuna godiya ga Li Keqiang da ya nuna kyakkyawan fata ga bikin nune-nunen a wannan karo, kuma ta bayyana cewa, kasar Sin abokiyar kasar Jamus ce mafi girma a fannin ciniki a nahiyar Asiya, kana ita ce muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa a fannin nazarin fasahohin zamani. Ta ce, Jamus da Sin suna da fifiko a fannin tattalin arzikin sadarwa, don haka kasashen biyu za su iya yin hadin gwiwa da samun moriyar juna a wannan fanni. (Zainab)