Yayin zantawar tasu Mr. Li Keqiang, ya bayyana cewa bangaren Sin yana mai da hankali sosai kan "shirin muradun kasa na shekarar 2040" wanda kasar Uganda ke fatan aiwatarwa, kuma za ta zabi kyawawan masana'antu domin dacewa da bukatun samar da ayyukan more rayuwar jama'a a kasar ta Uganda, ta yadda za ta bayar da gudummawar taimaka wa kasar, wajen bunkasa masana'antu, da zamanintar da kasar ta Uganda.
Mr. Li ya kara da cewa Uganda za ta iya samun dawaumammen ci gaba bisa karfin da take da shi. Sannan kasar Sin na fatan more fasahohin neman ci gaba tare da kasar Uganda, baya ga hadin gwiwa da take fatan yi da sauran kasashen gabashin Afirka, ciki har da kasar Uganda a fannin gina tsarin hanyoyin dogo a gabashin Afirka, ta yadda kasashen za su kai ga samun nasara, da kuma ci gaba tare.
A nasa bangare, Mr. Yoweri Museveni ya ce, kasar Sin ta dade tana goyon bayan kasashen Afirka a bangaren ci gaba ciki hadda kasar ta Uganda. Har wa yau kasar Uganda na maraba da kamfanonin kasar Sin wajen zuba jari a fannonin samar da makamashi, da takin zamani, da aikin sarrafa amfanin gona, da ayyukan samar da wutar lantarki ta ruwa.
A daya bangaren kuma, shugaban zaunannen kwamitin majalisar dokokin kasar Sin Mr. Zhang Dejiang, shi ma ya gana da Mr. Museveni a nan Beijing. (Sanusi Chen)