Shekarar bana shekara ce ta cika shekaru 70 na kafuwar kungiyar AL, kuma babban taken taron shugabannin kungiyar na wannan karo shi ne "shekaru 70 na kungiyar AL, a kiyaye tsaron kasashen".
Bugu da kari, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya halarci bikin bude taron, inda ya ba da jawabi cewa, rikice-rikice, yake-yake da kuma hare-haren ta'addanci na ci gaba da kasancewa a nan duniya, wadanda ba kawai suna kawo barazana ga tsaron yankin Larabawa, har ma kuma suna kasancewa babban kalubale ga zaman lafiya da tsaron kasa da kasa. Dalilin haka ne, Ban Ki-moon ya yi kira ga kungiyar AL da ta yi hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa, domin neman hanyar siyasa wajen warware wadannan matsaloli. (Maryam)