Bayan taron, majalisar kungiyar ta AL ta fidda wata sanarwa, inda ta nuna damuwa matuka game da tsanantar halin nuna karfin tuwo da ake ciki a kasar Libya. Kungiyar ta kuma jaddada cewa, tilas ne a girmama ikon mulkin kai, da 'yancin kai, da dinkewar kasar baki daya, da ma cikakken yankin kasar Libya, da bijirewa tsoma bakin kasashen waje ckan harkokin cikin gidan kasar.
Sanarwar ta bayyana cewa, wakilan kasashe mahalarta taron na ganin hanya daya tilo da ta dace a bi, domin warware matsalar Libya ita ce hanyar siyasa, bisa tushen cimma daidaito tsakanin kungiyoyin kasar daban daban. (Zainab)