in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta nacewa ka'idoji uku a kan hanyar samun ci gaba, in ji shugaban kasar Sin
2015-03-28 15:08:51 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya nanata burin kasar, na nacewa bin ka'idoji uku a kan hanyar neman cigaban kasar, ka'idojin da suka hada da tabbatar da bunkasuwar kasar Sin cikin lumana da tabbatar da bunkasuwar shiyyar baki daya da kuma tabbatar da hadin gwiwar kasashen Asiya da tekun Pasifik.

Hakan dai na kunshe ne cikin jawabin shugaba Xi a yayin taron Bo'ao na bana. Har wa yau shugaban kasar ta Sin ya bayyana cewa kasar sa ta shiga wani sabon hali na samun bunkasuwar tattalin arziki, bayan cimma nasarar samun ingantaccen ci gaba mai armashi a shekarar da ta gabata.

A daya hannun Xi ya ce kasar Sin za ta ci gaba da mai da hankali a kan kyautata ingancin tattalin arzikinta, tare da kara sanya muhimmanci a kan gyaran tsarin tattalin arzikin, don ciyar da tattalin arzikin kasar gaba.

Dadin dadawa, Mr Xi ya jaddada cewa, abin da Sin ke matukar bukata a halin yanzu shi ne yanayi mai karko da lumana a cikin gida da waje. Kasancewar tashe-tashen hankula, ko yake-yake ba zasu dace da moriyar jama'ar kasar Sin ba. Ya kuma bayyana cewa Sinawa ba su da burin ganin sauran al'umman duniya cikin mawuyacin hali, irin wanda suka taba jurewa a tarihi. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China