in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude taron shekara-shekara na tattaunawar Asiya na Boao
2015-03-28 13:05:09 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi, yayin bikin bude taron shekara-shekara, na tattaunawa tsakanin kasashen Asiya, da sanyin safiyar yau Asabar a birnin Bo'ao, wanda ke lardin Hainan a kudancin kasar Sin.

Cikin jawabin nasa, shugaba Xi ya bayyana cewa taron na wannan karo da aka yiwa lakabi da "Sabuwar makomar Asiya: Burin samun sabuwar makoma daya" ya dace da halin da ake ciki yanzu haka, kuma ya na da ma'ana kwarai a tsahon tarihi.

Shugaba Xi ya kuma yi fatan bangarori daban-daban, za su furta albarkacin bakinsu, da ba da shawarwarin samun zaman lafiya da bunkasuwar Asiya, da dama duniya baki daya.

Bisa tsarin wannan taro dai tun daga ranar 26 zuwa 29 ga wannan wata na Maris, za a aiwatar da ayyuka fiye da 70, a kuma tattauna kan wasu manyan batutuwa, ciki hadda na tattalin arziki a manyan fannoni, da hadin gwiwa tsakanin yankuna daban-daban, da kyautata tsarin masana'antu, da tsaron siyasa, da zaman rayuwar jama'a da dai sauransu.

Kaza lika mahalarta taron kimanin su 1700 daga kasashe daban-daban, za su yi shawarwari masu zurfi bisa jigon taron. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China