An sa ran Shugaban kasar Sin Xi Jinping zai halarci bikin kaddamar da taron,sannan kuma Shugabannin kasashen Armenia, serzh sarkisyan, da Austria, Heinz Fischer, da Uganda, Yoweri Museveni, da Zambiya, Edgar Lungu suna cikin wadansa zasu halarci wannan taro . Yawan shugabannin kasashen da za su halarci taron na bana ya wuce na shekarun baya, abin da ya shaida muhimmancin da suke sanyawa kan wannan taron.
A taron dandali na bana, za a gudanar da taruka 77 a hukunce a fannonin tattalin arziki daga manyan fannoni, da hadin gwiwa tsakanin shiyya-shiyya, da canza hanyar bunkasa masana'antu, da samar da sabbin fasahohi, da tsaron siyasa, da kyautata rayuwar jama'a da sauransu.(Fatima)