in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kafofin yada labarai na Sin da na ketare sun hadu a dandalin tattaunawar Asiya na Bo'ao
2015-03-26 20:31:10 cri
A yau Alhamis 26 ga wata, aka kira taron shugabannin kafofin yada labarai na taron shekara shekara na dandalin tattaunawar Asiya a garin Bo'ao na lardin Hainan da ke kudancin kasar Sin, inda shugabannin kafofin yada labarai sama da 20 daga kasashe 17, kamarsu Rasha, Amurka, Birtaniya suka halara., wadanda suka yi shawarwari kan batun yada labarai tsakanin al'adu iri daban daban, da hanyar hadin gwiwa da bunkasuwar kafofin yada labarai a nan gaba bisa taken "samar da makoma mai kyau ta hadin gwiwa tsakanin kafofin yada labarai bisa manufar bunkasa hanyar siliki ", tare da cimma matsaya a kan batutuwa da dama, da rattaba hannu kan yarjejeniyar hanyar siliki.

Shugaban taron, kana shugaban gidan rediyon kasar Sin CRI Wang Gengnian a jawabinsa ya mika fatan alheri ga mahalarta taron. Sannan suma sauran mahalartan a cikin jawabansu sun bayyana fatansu cewa, kafofin yada labarai za su kara hadin gwiwa tsakaninsu, da bayar da fasahohi da horar da ma'aikata, da fatan za a kafa kungiyar hadin gwiwar kafofin yada labarai a lokaci mai dacewa da sauransu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China