in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kai ga tsara takardar manufar yanki da hanyar Siliki,inji shugaban kasar Sin
2015-03-28 14:47:55 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya jinjinawa dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, bisa jajircewar su wajen tsara takardar manufar "yanki da hanyar Siliki".

Shugaban na Sin ya bayyana hakan ne cikin jawabin da ya gabatar ga mahalarta taron Bo'ao na bana.

Ya ce tsarin "yanki da hanyar Siliki" na da ma'anar gaske wajen ci gaban kasar Sin, da kuma sauran kasashen da ke kan wannan ziri, da ma daukacin yankin baki daya. A daya hannun tsarin zai zamo mai alfanu ga daukacin sassan masu ruwa da tsaki, baya ga kasancewar sa jigo, wajen biyan bukatun yankin, da kuma daukacin duniya baki daya.

Tsarin "yanki da hanyar Siliki" mai kunshe da manufofin bunkasa tattalin arzikin yankin da tsohuwar hanyar siliki ta ratsa, da kuma bunkasa hanyar siliki ta ruwa a karni na 21, tsari ne da shugaba Xi ya gabatar a shekarar 2013, lokacin da yake ziyarar aiki a kasashen Kazakhstan da Indonesia.

Manufar bunkasa tattalin arzikin yankin Siliki dai ita ce habaka zirin cinikayya, wanda zai game daukacin yankunan Arewa maso Yammacin kasar Sin zuwa tsakiyar nahiyar Asiya da turai, yayin da kuma manufar bunkasa hanyar siliki ta ruwa a karni na 21, za ta shafi sassan yankunan Kudancin kasar Sin zuwa Kudu maso Gabashin Asiya, da ma yankunan nahiyar Afirka.

Ana sa ran kammalar wannan kuduri zai amfani mutanen da yawan su ya kai biliyan 4.4, kimanin kaso 63 bisa dari ke nan na daukacin al'ummar duniya.

Ya zuwa yanzu, sama da kasahen duniya 60, da hukumomin kasa da kasa da dama ne suka nuna sha'awar su, ta shiga a dama da su cikin wadannan manufofin ci gaba biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China