Yayin da yake ganawa tare da Mr. Vuk Jeremic, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, babban nauyi ne ga MDD, batun kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa, kasar Sin ita ce muhimmiyar abokiya ga MDD kan wannan aiki, kuma za ta ci gaba da ba da taimako ga kasashe masu tasowa, don karfafa matsayansu cikin harkokin kasa da kasa.
Yayin da yake ganawa tare da Mr. Lagarde kuwa, shugaba Xi ya nuna cewa, a halin yanzu, yanayin tattalin arzikin duniya na ci gaba da bunkasa, tare da fuskantar kalubaloli da dama, ya kamata gamayyar kasa da kasa su karfafa gyare-gyaren maufofin tattalin arziki, don ba da taimako ga kasashe masu tasowa wajen kawar da talauci, da cimma burin ci gaba cikin tsawon lokaci.
Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan ayyukan kwaskwarimar Asusun ba da lamuni na IMF.
A shawarwari da ya yi tare da Mr. Gates kuwa, Mr. Xi Jinping ya nuna cewa, kasar Sin na fatan yin hadin gwiwa tare da asusunsa, don dukufa tare wajen ciyar da zaman lafiyar al'ummomin duniya gaba, da kuma kawar da talauci. (Maryam)