Gidan rediyon kasar Sin CRI da hadin gwiwwar hukumar birnin Sanya da gidan rediyo da na talibijin din birnin Sanya ya gudanar da bikin nune-nunen hotuna mai taken "Kyakkyawan shimfidar wuri na nahiyar Asiya a hotuna na shekarar 2015" kuma bikin yin musayar al'adu kan jigon "Hanyar siliki" a yau Juma'a 27 ga wata a birnin Sanya dake kudancin kasar Sin.
Sabon bikin nuna hotuna a wannan karo ya gabatar da shimfidar wuri mai kayatarwa da al'adu masu ban sha'awa a nahiyar Afrika, tare kuma da hada shi da taken dandalin tattaunawar Asiya na Bo'ao da ke gudana yanzu haka wato "Sabuwar makomar Asiya: Burin samun sabuwar makoma daya", hakan hotuna sun bayyana mu'amalar al'adu tsakanin kasashen daban-daban a Asiya, musamman ma sabuwar bunkasuwa, sauye-sauye da Asiya ke samu a cikin shekara da ta gabata, wadanda kuma sun samun karbuwa sosai daga mahalartan bikin. (Amina)