Mr Hong yace Sin ta damu matuka game da yuwuwar daukan matakan soja da wassu kasashe ke son yi a kasar,yana mai nuni da cewa duk wani mataki da za'a dauka ya kamata ya tafi da tsarin kundin MDD da kuma sauran ka'idoji na sauran kasashen duniya domin kaucewa tsanantar yanayin da ake ciki a kasar Sham da sauran kasashen yankin gabas ta tsakiya.
Mr Hong yace Sin tana kara jaddada goyon bayan ta da a aiwatar da bincike mai zaman kansa a bayyane ba bisa wani ra'ayi ba sai adalci wanda da MDD ta riga ta nada kwararrun jami'ai a wannan fanni na bincike makamai masu guba don aiwatarwa.
Bai kamata a yanke shawara kafin a bayyana sakamakon kwamitin binciken ba,inji Mr Hong. (Fatimah Jibril)