in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin kasar Sin ya yi kira ga bangarori daban-daban na Yemen da su warware rikici ta hanyar shawarwari
2015-02-13 16:20:05 cri

Wakilin dindindin na kasar Sin a MDD Liu Jieyi , wanda kuma yake rike da shugabancin kwamitin sulhu na majalisar a wannan karo ya bayyana cewa, yana fatan bangarori daban-daban na kasar Yemen za su warware rikicin ta hanyar shawarwari tsakaninsu tare da la'akarin da moriyar kasa da jama'arsu.

Mr Liu ya jagorancin wani taron da kwamitin ya yi kan batun kasar Yemen, bayan taron ya bayyana cewa, mambobin kwamitin na mai da hankali sosai kan halin siyasa da kasar Yemen ke ciki, tare da nanata cewar ya kamata a tabbatar da cikakken yanki, dunkulewa da mulkin ikon kasar, tare da yin kira ga bangarori daban-daban a Yemen musamman ma kungiyar Houthi da su bi shawarar kwamitin hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a Gulf Persia, takardun da aka cimma a shawarwarin tsakanin bangarori daban-daban a kasar, da yarjejeniyar abokantaka ta zaman lafiyar al'umma, ta yadda za a ci gaba da sa kaimi ga samu bunkasuwa a siyasance a kasar, da goyon bayan shiga tsakanin da manzon musamman na MDD mai kula da harkokin Yemen Jamal Benomar ya yi, kuma ya maraba da hukumomin da wannan abin ya shafa a yankin da kasashe dake makwabtaka da Yemen da su ba da gudunmawar su wajen sa kaimi ga warware rikicin Yemen cikin lumana.

Kazalika, Mr Liu ya ce, akwai zumunci mai karfi tsakanin Sin da Yemen, don haka Sin na fatan bangarori daban-daban na Yemen za su mai da hankali kan moriyar kasar da jama'ar su, kana da kara hada kai da yin shawarwari wajen kawar da bambanci a tsakaninsu, da kuma ci gaba da inganta yunkurin wucin gadi a fannin siyasa, da sake farfado da kasar tun da wuri. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China