A gun bikin daddale yarjejeniyar, manzon musamman na MDD mai kula da batun Yemen Gamal bin Omar ya sanar da abubuwan da aka rubuta cikin yarjejeniyar. Ya ce gwamnatin kasar Yemen da kungiyar dakaru ta Houthi sun amince da tsaigaita bude wuta a birnin Sanaa ba tare da bata lokaci ba. Haka kuma Shugaban kasar Abdrabuh Mansur Hadi zai nada sabon firaministan kasar, kana za a kafa gwamnatin kasar dake kunshe da jami'ai masana, sannan za a rage farashin man fetur. Yarjejeniyar ta kara bada iko ga kungiyar Houthi yayin da ake kafa majalisar ministoci da yin kwaskwarimar sojojin kasar a nan gaba.
Amma kungiyar Houthi ta ki amincewa da sashen tsaro dake cikin yarjejeiyar, inda aka bukaci da ta mika biranen da ta mallaka ga gwamnatin kasar,tare da janye dukkan dakaru daga birnin Sanaa, da dakatar da yin zanga-zanga, da kuma ajiye makamai bisa yarjejeniyar samun sulhuntawa a kasar.
Bisa labarin da kamfanin dillancin labaru na SABA na kasar ya bayar, an ce, firaministan kasar Yemen Mohammed Salim Basindwa ya sanar da yin murabus kafin aka daddale yarjejeniyar tsagaita bude wutar. (Zainab)