in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Birtaniya da Amurka da Faransa sun janye ma'aikatan jakadancinsu daga kasar Yemen
2015-02-12 14:52:48 cri
Ofisoshin jakadancin Birtaniya da Amurka da Faransa dake kasar Yemen sun sanar a ranar 11 ga wata cewa, sun dakatar da ayyukan jakadancinsu tare da kwashe ma'aikatansu a sakamakon rashin tsaro da halin rudani da kasar Yemen ta shiga.

Haka zalika kuma, ofisoshin jakadancin kasashen uku sun bukaci jama'arsu da su janye daga kasar Yemen cikin hanzari.

A ranar 11 ga wata, ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta yi kira ga kungiyar dakarun Houthi ta darikar Shi'a ta kasar Yemen dake mallakar birnin Sanaa na kasar Yemen da ta saki shugaban kasar Yemen da ministocin kasar da ta yi garkuwa da su. Kana ta bayar da sanarwa a wannan rana cewa, dukkan jama'ar kasar Yemen suna da iko da alhakin shiga tattauna kan makomar kasarsu cikin lumana. Idan aka ci gaba da yin garkuwa da shugaban kasar da ministocin kasar, to akwai wuya a warware rikicin siyasar kasar . (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China