Sanarwar ta bayyana cewa, mashawarcin musamman na babban sakataren MDD Jamal Benomar zai sake yin kira ga bangarori daban daban da batun kasar Yemen ya shafa da su yi shawarwari a ranar 9 ga wata, Ban Ki-moon ya yi maraba da wannan batu, tare da kalubalantar bangarorin da su yi hadin gwiwa tare da Jamal Benomar domin nuna dattako a gun shawarwarin.
Kungiyar dakarun Houthi ta darikar Shi'a ta kasar Yemen ta sanar da kafa kwamitin kula da harkokin shugaban kasar da majalisar gudanarwa ta wucin gadi ta kasar a ranar 6 ga wata, don maye gurbin shugaban kasar na yanzu da majalisar dokokin kasar da gudanar da harkokin kasar. Matakin na kungiyar Houthi ya sanya kasar cikin wani halin rudani da rashin tabbas game da rashin wata gwamnatin kasar mai cikakken iko. (Zainab)