Magatakardan MDD Ban Ki-moon ya yi na'am da sanarwar da aka gabatar ta kafa wata sabuwar gwamnati a kasar Yemen, inda ya ce, wannan mataki, wani albishir ne na kaiwa ga tsarin siyasa mai dorewa da kuma zaman lafiya a kasar ta Yemen.
Magatakardan MDD wanda ya yi jawabin nasa a cikin wata sanarwa wacce ta fito daga kakakin shi, ya ce, ya yi lale marhabin da kafa gwamnatin zaman lafiya da hadin gwiwa a kasar Yemen, musamman a daidai wannan lokaci na taka tsan-tsan, kuma yana mai fatan hakan zai haifar da zaman lafiya a kasar.
Tun farko a ranar Jumma'a ne aka bayar da sanarwar kafa sabuwar gwamnati a kasar Yemen, bayan an sha fuskantar matsalar rikice-rikice na siyasa saboda arangama tsakanin kungiyoyi masu adawa da juna.
Jiga-jigan masu adawa 'yan tsageran Houthi, a ranar Asabar din da ta gabata ne suka rattaba hannu a kan wata yarjejeniya da ta umurci shugaban kasar da firaministansa da su kafa sabuwar gwamnati.(Suwaiba)