in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da kasar Yemen ke ciki ya kara tsananta
2015-02-07 17:14:33 cri
Kungiyar Houthi ta mabiya darikar shi'a a kasar Yemen, ta sanar da kafa kwamitin shugabanci da na wucin gadin kasar, domin maye gurbin shugaba, da majalisar dokokin kasar da ta hambarar. A daidai gabar da yanayin tsaro ke dada tabarbarewa a kasar.

Kungiyar ta bayyana hakan ne yayin wani taron manema labaru da ta kira a jiya Juma'a a birnin Sana'a fadar gwamnatin kasar.

Ana dai danganta rikice-rikice, da zanga-zanga dake faruwa a kasar ta Yemen, da hambarar da gwamnatin da kungiyar ta Houthi ta yi, wanda hakan ya haifar da rashin gwamnati a kasar.

A ranar 19 ga watan Jarairun da ya shude ne wasu magoya bayan Houthi dauke da matakai, suka aukawa cibiyoyin gwamnati, da jami'an tsaron kasar, ciki hadda rundunar dake tsaron shugaban kasar, inda suka mamaye fadar gwamnatin.

Daga bisani shugaban kasar Abdu Rabbih Mansour Hady, da firaminista Khaled Bahah sun sanar da yin murabus daga mukamansu, kuma majalisar dokokin kasar ta sanar da dage lokacin zartas da takardun barin aikin shugabannin.

Masu fashin baki na ganin matakin da kungiyar ta dauka ya haifar da babbar matsala ta rashin takamammiyar gwamnati, baya ga rikici tsakanin kabilun kasar daban-daban da hakan ya janyo.

Kaza lika hakan ya baiwa kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi kamar Al-Quaeda, samun damar shiga kasar domin karfafa ikonsu, matakin da ke dada tsananta halin da kasar ta Yemen ke ciki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China