Bisa labarin da ma'aikatar harkokin waje ta kasar Amurka ta bayar, an ce, rahoton yiwuwar kai harin ta'addanci daga reshen kungiyar al-Qeada a zirin kasashen larabawa, ya sa za a ci gaba da rufe ofishin jakadancin na Amurka dake kasar ta Yemen. A halin yanzu, ana ci gaba da yin kokarin tabbatar da tsaro a ofishin jakadancin yake, ana ci gaba da kuma jibge sojojin kota-kwana da tankuna domin bada karayi ga ofishin jakadancin. (Zainab)