Kamfanin dillancin labaru na gwamnatin kasar Yemen ya bayar da wani labari a ran 5 ga wata cewa, wani mai aikin tsaro 'dan Faransa ya mutu yayin da wani bafaranshe guda ya ji rauni sakamakon wani harin da kungiyar Al-Qaida ta kai a Sanaa, babban birnin kasar.
Labarin ya ruwaito maganar wani jami'in ma'aikatar kula da harkokin cikin gida ta kasar cewa, an kai farmakin ne a wani wurin da ke dab da ofishin jakadancin Faransa da ke Yemen, bayan haka dakarun sun tsira daga wurin. Hukumomin da abin ya shafa na gudanar da bincike kan batun, haka ma an riga an kai mutumin da ya ji rauni zuwa asibitin da ke kusa.
A cikin wata sanarwa a ran 5 ga wata, kwamitin sulhu na MDD ya yi alla wadai da wannan harin ta'addanci, tare da sake jaddada goyon baya ga gwamnatin Yemen wajen yaki da ta'addanci.
Sanarwar ta cigaba da cewa, matsalar ta'addanci ta kasance daya daga cikin abubuwan da suka fi kawo barazana ga zaman lafiya da tsaron duniya. Ko wane lokaci ko wane wuri, ko wace hujjar da ake gudanar da ta'addanci, to, dukkansu babban laifi ne. (Danladi)