in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An aiwatar da dokar-hana-fitar-dare a wasu wuraren hedkwatar kasar Yemen
2014-09-21 17:00:42 cri

Ranar 20 ga wata, dakarun Hussain na darikar Shia da sojojin gwamnatin kasar da mayakan darikar Sunni suna ci gaba da musayar bude wuta a tsakaninsu a birnin Sanaa, hedkwatar kasar Yemen. Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Yemen ta sanar da aiwatar da dokar-hana-fitar-dare tun daga ranar 20 ga wata a wasu wuraren da ke arewa maso yammacin Sanaa, inda aka fi samun kazamin fada.

Hartsigin da aka kwashe kwanaki da dama ana yinsa ya tilasta wa dubban fararen hular da ke zaune a arewacin Sanaa ficewa daga gidajensu. Ma'aikatar ilmi ta Yemen ta sanar da dakatar da karatu a makarantun firamare da na midil a duk fadin birnin Sanaa tun daga ranar 21 ga wata, yayin da jami'ar Sanaa ta sanar da rufe kofa tun daga ranar 20 ga wata.

Jamal bin Omar, manzon musamman na MDD mai kula da batun Yemen ya bayyana a wani taron manema labaru a daren ranar 20 ga wata a Sanaa cewa, gwamnatin Yemen da dakarun Hussain na darikar Shia sun cimma daidaito kan tanade-tanaden da ke cikin yarjejeniyar tsagaita bude wuta. Amma bai ce kome ba dangane da daidai lokacin da bangarorin 2 za su daddale yarjejeniyar.

Rikicin siyasa a wannan karo ya barke ne saboda gwamnatin Yemen ta rage kudin alawas ta fuskar mai. Ranar 30 ga watan Yuli gwamnatin Yemen ta sanar da daga farashin man fetur da dizal, lamarin da ya janyo bacin ran fararen hula, lamarin da ya sanya dakarun Hussain na darikar Shia da sauran 'yan hamayya su jagoranci al'ummar kasar wajen gudanar da zanga-zanga tun daga farkon watan Agusta har zuwa yanzu. (Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China