150122-an-bude-gasar-cin-kofin-kwallon-kafar-nahiyar-afirka-ta-2015-zainab.m4a
|
Kamar dai yadda mai sauraro ya sani, a ranar Asabar din da ta gabata ne aka bude gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka ta bana a kasar Equatorial Guinea.
Inda yayin wasan bude gasar da ya gudana tsakanin mai masaukin baki Equatorial Guinea, da Congo Brazzaville, aka tashi 1 da 1 a filin wasa na Bata.
Lopez Emilio Nsue wanda ke wasa a kulaf din Middlebrough FC na kasar Ingila ne ya ciwa Equatorial Guinea kwallon farko cikin minti na 16.
Congo ta yi matukar kokarin farke kwallon da aka zura mata amma hakan ta farkara. Ana kuma daf da tashi daga wasan ne dan wasan Congo Thievy Bifouma Koulossa, ya jefa kwallo a ragar Equatorial Guinea, aka kuma tashi 1 da1.
"Yan kallo 30,000 ne dai, ciki hadda shugaban kasar Equatorial Guinea Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, da shugaban hukumar kwallon kafar Afirka Issa Hayatou suka kalli wasan na farko.