An dai rika rade radin komawar Abreu, dan shekaru 38 zuwa tsohon kulaf din na sa, bayan wata ganawa da ya yi da wasu jami'an kulaf din cikin makon da ya gabata.
Manajan kulaf din na Botafogo Antonio Lopes ya bayyanawa 'yan jaridu cewa, babu wani shiri na dawowar wannan dan wasa a halin yanzu.
Shi dai Abreu ya kasance daya daga 'yan wasan Botafogo daga shekarar 2010 zuwa 2012, ya kuma samu karbuwa wajen magoya bayan kungiyar, bayan da ya taimakawa kungiyar lashe kofin kwararru na Rio de Janeiro a kakar farko da ya yi a kungiyar.
Yanzu haka dai Abreu ya kammala kwantiragin sa da Rosario Central na kasar Argentina a farkon watan nan.
A bana Kulaf din Botafogo dai zai buga gasar aji na biyu na kulaflikan kasar Brazil, bayan da ya kasance a matsayi na biyun karshe a gasar ajin kwararru ta bara.
Kaza lika kulaf din ya maye gurbin kocin sa Vagner Mancini da sabon koci Rene Simoes. Sabon kocin na Botafogo shi ne ya jagoranci kungiyar kasar Jamaica zuwa gasar cin kofin duniya na farko da ta halarta a shekarar 1998. (Saminu Alhassan)