in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nyambe Mulenga na Zambiya ba zai buga gasar cin kofin Afirka ba
2014-12-23 10:02:03 cri
Dan wasan baya na kasar Zambiya Nyambe Mulenga, ba zai buga gasar kwallon kafar nahiyar Afirka da kasar Equitorial Guinea za ta karbi bakunci ba, sakamakon jiyyar makwanni 12 da zai yi.

Mulenga ya samu rauni ne a hannu da kafar sa, ya yin wani hadarin mota da ya ritsa da 'yan wasan kasar ta Zambia, lokacin da suke kan hanyar halartar sansanin horas da tawagar kwallon kafar kasar.

Dan wasan mai shekaru 33 da haihuwa wanda kuma ke bugawa kulaf din Zesco United kwallo, ya taka rawar gani a wasannin da suka baiwa kasar gurbin buga gasar cin kofin Nahiyar Afirka, wanda za a buga daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi.

Tuni dai kocin kungiyar Honor Janza ya gayyaci wasu 'yan wasa na gida, domin cike gurbin dake akwai, ya yin da kuma ake sa ran zai fidda sunayen 'yan wasan dake waje, da za su bugawa kungiyar cikin mako mai zuwa.

Kungiyar kasar Zambia Chipolopolo dai za ta buga wasannin zagayen farko na gasar cin kofin Afrikan ne a rukuni na biyu, tare da kulaflikan kasashen janhuriyar dimokaradiyyar Congo, da Cape Verde da kuma Tunisia.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China