in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An bude gasar cin kofin kwallon kafar nahiyar Afirka ta 2015
2015-01-23 09:03:37 cri

Kidiaba na Congo ya yi farin cikin zama dan wasa mafi dadewa yana buga gasar cin kofin Afirka

Mai tsaron gidan kungiyar kwallon kafar janhuriyar dimokaradiyyar Congo Robert Muteba Kidiaba, ya ce yana matukar farin cikin kasancewar sa dan wasan da ya fi kowa dadewa, yana halartar gasar cin kofin Afirka.

Kidiaba wanda ya shahara wajen kare kwallaye, da nuna matukar murna a duk lokacin da kungiyar sa ta samu nasara, zai cika shekaru 39 da haihuwa a ranar 1 ga watan Fabarairun dake tafe.

Mai tsaron gida Kidiaba ya taimakawa kulaf din TP Mazembe wajen lashe kofin zakarun kasar Congo. A wannan karo kuma ya bayyana fatan tallafawa kasar sa lashe kofin Afirka da ake bugawa a yanzu haka. Kidiaba yace su na matukar burin daukar wannan kofi, duk kuwa da cewa hakan ba abu ne mai sauki ba.

Da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarun kasar Sin Xinhua, game da kasancewar sa dan wasa mafi tsufa a wannan gasa, Kidiaba ya ce yana ci gaba da aiki tukuru, kuma wannan shekara ma tana da muhimmancin gaske gare shi, kasancewar har ya zuwa yanzu, ya na jin dadin taka leda matuka.

Janhuriyar dimokaradiyyar Congo dai na rukuni na B tare da Zambia, da Tunisia da kuma Cape Verde. Ta kuma taba lashe wannan kofi sau daya a shekarar 1968.

Rahotanni daga hukumar CAF na nuna cewa cikin jimillar 'yan wasa 368 da suka halarci gasar ta bana, 'yan wasa 26 ne kadai suka haura shekaru 30. Kana mai tsaron gidan kasar Kamaru na uku, Pierre Sylvain Abogo ne dan wasa mafi karancin shekaru, inda a ranar 27 ga watan nan na Janairu zai cika shekaru 17 da haihuwa.

Bisa tarihi dai wannan ne karo na 30 da ake buga wannan gasa ta cin kofin Afirka, inda kasar Masar ta kasance mafi daukar kofin da kofuna 7. Sai kasar Ghana da Kamaru, da suka dauki kofin sau hurhudu. Najeriya ta dauka sau 3, yayin da janhuriyar dimokaradiyyar Congo ta dauka sau 2. Sai dai a bana Najeriya dake rike da kambin gasar da aka buga a shekarar 2013 ta gaza samun tikitin zuwa gasar. (Saminu Alhassan)


1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China