in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Liverpool ya tabbatar da komawar Gerrard MLS na Amurka
2015-01-08 15:15:45 cri
Mahukuntan kulaf din kwallon kafar Liverpool, sun ce kwaftin din kungiyar Steven Gerrard zai koma kulaf din MLS na Amurka, bayan kammala buga kakar wasannin bana.

Tun a ranar Juma'ar da ta gabata ne dai Gerrard mai shekaru 34 da haihuwa, ya bayyana aniyar sa ta barin Liverpool, bayan ya kwashe shekaru 25 ya na taka leda a kulaf din. Inda ya buga wasanni 695, ya kuma ci kwallaye 180.

Rahotanni daga wasu kafofin watsa labaru sun bayyana cewa, mai yiwuwa ne Gerrard na son bin sahun takwaransa David Beckham ne, wanda ya koma Los Angeles Galaxy daga Manchester United, a karshe karshen sana'ar sa ta kwallon kafa. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China