in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Real Madrid ta doke Cruz Azul a wasan cin kofin zakarun nahiyoyi
2014-12-23 10:02:55 cri
Kulaf din Real Madrid na Sifaniya ya lallasa Cruz Azul na Mexico da ci 4 da nema, a wasan kusa da na karshe na cin kofin zakarun nahoyoyi da suka buga a ranar Talatar da ta gabata.

Hakan dai na zuwa ne ya yin da Madrid din ke kara yawan wasannin da ta lashe, wadanda ya zuwa yanzu suka kai wasanni 21 a jere, bayan wasan na birnin Marrakech.

'Yan wasan kungiyar Sergio Ramos, da Karim Benzema ne dai suka bude wa Madrid zura kwallaye, kafin daga bisani Bale da Isco su kammala ciwa kulaf din kwallaye.

Yanzu dai haka Real Madrid din na jiran buga wasan karshe na wannan gasa a ranar Asabar a filin wasa na birnin Marrakech.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China