Gabon ta doke Burkina Faso 2-0
A ci gaba da wasannin cin kofin nahiyar Afirkan, kasar Gabon ta doke Burkina Faso da ci 2 da nema a wasan su na ranar Asabar.
Da wannan sakamako ne kuma Gabon din ta dare matsayi na faro a rukunin A.
Kasar Gabon dai ta kai wasan kusa, da kusan na karshen a gasar da ta gudana a shekarar 2012.
Dan wasan kasar ta Gabon Pierre-Emerick Aubameyang dake taka leda a kasar Jamus ne ya fara saka kwallo a ragar Burkina Faso cikin minti na 19. Kafin daga bisani bayan dawowa hutun rabin lokaci Malick Evouna ya kara kwallo ta biyu ga Gabon.
Yanzu haka dai Gabon na matsayi na 62 a duniya, cikin kulaflika mafiya kwarewa a fagen tamaula, kuma alamu na nuna burin kungiyar kasar na daga matsayin ta a gasar ta wannan karo.
Sauran wasannin da aka buga a makon sun hada da wasan rukunin B, inda a ranar Lahadi 18 ga wata, Tunusia ta tashi kunnen doki daya da daya ita da Cape Verde. Haka ma aka tashi wasan Zambia da Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo daya da daya.
A ranar Litinin kuma wasannin rukunin C Ghana ta sha kashi hannun Senegal da ci 2 da 1, ya yin da ita kuma Algeria ta lallasa Afirka ta Kudu da ci 3 da 1.
Sai wasan ranar Talata rukuni na D, inda Cote d'Ivoire ta buga kunnen doki 1 da 1 ita da kasar Guinea. Haka ma wasan da Mali ta buga da Kamaru, shi ma an tashi ne 1 da 1.