in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yaya Toure ya zama gwarzon dan kwallon nahiyar Afirka na shekarar 2014
2015-01-23 09:01:45 cri
Hukumar shirya gasannin kwallon kafar Afirka CAF, ta bayyana sunan dan wasan kasar Cote d'Ivoire Yaya Toure, a matsayin gwarzon dan kwallon nahiyar Afirka na shekarar 2014.

Yaya Toure ya doke sauran 'yan takarar wannan matsayi da suka hada da dan wasan Gabon Pierre Emerick Aubameyang, da dan mai tsaron gidan Najeriya Vincent Enyeama. Kana wannan ne karo na hudu a jere, da Yaya Toure ya cimma nasarar samun wannan lambar yabo.

Yaya Toure ya ci kwallaye 20 a wasanni 35 da ya bugawa kungiyar Manchester City a kakar wasa ta shekarar 2013 zuwa 2014, matakin da ya taimakawa kungiyar, samun nasara a gasar Firimiya.

Nasarar da ya samu ta lashe lambar yabo ta gwarzon dan kwallon nahiyar Afirka a wannan karo, ta sanya Toure kamo dan wasan kwallon kasar Kamaru Samuel ETO'O, a yawan samun wannan lamba sau 4 a jere.

A daya bangaren kuma, dan wasan kasar Portugal Cristiano Ronaldo, ya doke Lionel Andrés Messi daga kasar Argentina, da dan wasan kasar Jamus Manuel Neuer, a matsayin gwarzon dan kwallon duniya na shekarar 2014.

Yaya Toure: Cote d'Ivoire ce za ta lashe gasar cin kofin Afirka a wannan karo

Shahararren dan wasan kasar Cote d'Ivoire Yaya Toure ya ce ko shakka ba bu, kasar sa ce za ta dauki kofin gasar kwallon kafan Afirka na wannan karo.

Yaya Toure ya bayyana hakan ne ga manema labaru a 'yan kwanakin baya, yana mai cewa kasar na da burin sake lashe wannan kofi, duk kuwa da cewa akwai kungiyoyi masu karfi da dama da suke da aniyar lashe kofin na bana. Ya ce babu shakka za su yi kokarin cimma wannan buri na su.

Cote d'Ivoire dai za ta buga wasanni da kungiyoyi masu karfi kamar Ghana, da Algeria, da Senegal dake da taurarin 'yan wasa da dama. Sai dai a cewar Toure abin bakin ciki ne da Nijeriya ba ta samu zuwa gasar ta bana ba.

Cote d'Ivoire dai na cikin rukuni na D tare da Kamaru, da Guinea, da kuma Mali. Kuma a baya ta taba lashe gasar cin kofin Afirka a shekarar 1992, gasar da aka buga a kasar Senegal. Kana ta samu matsayi na kungiya mafi karfi, da mafi samun damar cin kofin a lokuta da dama, duk da cewa a shekarar 1992 ne kadai ta samu damar lashe gasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China