A jiya ne shugaba Peter Poroshenko na kasar Ukraine ya ce, zai yi shawarwari da takwaransa na kasar Faransa Francois Hollande, da na kasar Rasha Vladimir Putin da kuma shugabar gwamnatin kasar Jamus madam Angela Merkel a kasar Kazakhstan a ranar 15 ga watan Janairu a shekara mai zuwa, inda za su tattauna yadda za a warware rikicin Ukraine.
Dangane da lamarin, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a nan Beijing yau Talata 30 ga wata cewa, kasar Sin na maraba da kuma goyon bayan kokarin da bangarori masu ruwa da tsaki suke yi na warware rikicin Ukraine a siyasance. Kasar Sin ta kuma bukace su da su cimma daidaito cikin hanzari, a kokarin warware rikicin tare. (Tasallah)