An labarta cewa, a kwanan baya shugaba Vladimir Putin na kasar Rasha ya ce, kasarsa ta riga ta janye sojojinta daga bakin iyakar kasashen Rasha da Ukraine, kuma Rasha za ta rubanya kokarinta na warware rikicin Ukraine.
Dangane da hakan, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana yau Jumma'a 9 ga wata a nan Beijing cewa, kasar Sin na maraba da kokarin da sassa daban daban masu ruwa da tsaki suke yi wajen warware rikicin a siyasance. Tana kuma goyon bayan matakan da za a ci gaba da dauka wadanda za su taimaka wajen sassauta halin da ake ciki yanzu, da kuma kara azama kan warware rikicin ta hanyar siyasa. (Tasallah)