Breedlove wanda ke ziyara a kasar Ukraine ya kuma bayyanawa manema labaru cewa, kasar Amurka ta gudanar da bincike kan bukatun sojojin kasar Ukraine, an kuma gwada dukkan yiwuwar samar da gudummawa ga sojojin na Ukraine.
Ya ce Ukraine na fuskantar kalubale mai tsanani, don haka kasar Amurka ta shirya ba ta dukkanin tallafin da ya dace.
Ban da wannan, Breedlove ya bayyana cewa, yanzu haka kasashen duniya na kokarin taimakawa Ukraine, da neman hanyar diplomasiyya wajen tabbatar da mulkin kai, da cikakken yankin kasar.
Kaza lika kasar Amurka za ta ci gaba da mu'amala tare da shugabannin kasar ta Ukraine, in ji mista Breedlove. (Zainab)