Dangane da halin da ake ciki yanzu a kasar Ukraine, madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, kasar Sin na mai da hankali sosai kan halin da ake ciki a Ukraine, tana fatan bangarori daban daban masu ruwa da tsaki a Ukraine za su ci gaba da daidaita rikicin kasar cikin ruwan sanyi ta hanyar yin shawarwarin siyasa bisa doka, a kokarin samun kwanciyar hankali a harkokin siyasar kasar, da maido da doka da oda a kasar cikin sauri.
Madam Hua ta fadi haka ne a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing yau Litinin 24 ga wata. Ta kara da cewa, Sin ba ta tsoma baki cikin harkokin cikin gida na Ukraine. Tana girmama zabin da jama'ar Ukraine za su yi bisa halin da kasarsu take ciki. Tana son ci gaba da raya huldar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakaninta da Ukraine bisa ka'idar yin zaman daidai wa daida da samun moriyar juna. (Tasallah)