An yi shawarwarin ne ba tare da gayyatar 'yan jarida ba, kana mahalartar taron ba su yi wani bayani game da abubuwan da suka tattaunawa a gun shawarwarin ba. Shawarwarin kuma da ya samu halartar wakilai da suka fito daga jihohin Luhansk da Donetsk.
Kamfanin dillancin labaru na kasar Belarus ya bayyana cewa, ba abin da ya canja game da abubuwan tattauna a shawarwarin, muhimman batutuwan da aka tattauna sun hada da matsayin yankunan biyu na gabashin kasar Ukraine, janye manyan makamai daga yankin, musayar mutanen da aka yi garkuwa da su, jigilar kayayyakin jin kai zuwa yankin dake hannun 'yan tawaye da dai sauransu.
Manazarta na ganin cewa, duk da cewa ba a aiwatar da yarjejeniyar da aka daddale baya ba, bangarori daban daban da abin ya shafa sun nuna kyakkyawan fata ga shawarwarin na wannan zagaye, kana suna fatan za a cimma sabuwar yarjejeniya a birnin Minsk kafin karshen shekarar 2014, ta yadda za a inganta warware rikicin na Ukraine. (Zainab)