Klimkin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a wannan rana cewa, kasar Ukraine ta shirya gudanar da taron bangarori uku wato Ukraine, kungiyar tsaro da hadin gwiwa ta Turai (OSCE), da kuma Rasha don tattauna batun rikicin Ukraine.
Ministan harkokin wajen kasar Ukraine ya yi nuni da cewa, yadda za a aiwatar da yarjejeniyar Minsk da aka daddale a watan Satumba shi ne muhimmin abin da za a tattauna a gun taron.
Wakilin kungiyar OSCE Heidi Tagliavini ya bayyana a birnin Kiev a wannan rana cewa, rukunonin yin mu'amala na bangarorin uku za su tattauna batutuwan tsagaita bude wuta, janye manyan makamai daga yankin, musayar mutanen da aka yi garkuwa da su, jigilar kayayyakin jin kai zuwa yankin dake hannun 'yan tawaye da dai sauransu.
Shugaban "jamhuriyyar Donetsk" Alexander Zakharchenko ya bayyana cewa, ba shi da masani game da ganawar da za a yi a birnin Minsk a ranar 24 ga wata. Sai dai wakilin "jamhuriyyar Luhansk" ya bayyana cewa, zai je birnin Minsk, don ganin an shigar da dokar matsayin musamman na yankin Donbas da dokar yin afuwa a cikin tattaunawar da za a yi. (Zainab)