A ganawarta da manema labarai a nan birnin Beijing Madam Hua tace kamata ya yi, kwamitin sulhun ta mai da hankalinta kan harkokin kiyaye zaman lafiya da na karko a duniya.
Madam Hua Chunying ta ce, yanzu halin da zirin Korea ke ciki a yamutse yake sosai, don haka kasar Sin na fatan mambobin kwamitin da bangarori daban-daban dake da nasaba da wannan batu su sa kaimi ga aikin kawar da makaman nukiliya da kuma kiyaye zaman lafiya da na karko a zirin, sannan kuma a dauki matakan da suka dace don sassauta halin da ake ciki a zirin, da hana a fitar da matakai ko zance da zai tada zaune tsaye.
Madam Hua ta nanata cewa, kullum kasar Sin ba ta yarda da mai da batun hakkin dan Adam a siyasance, ko matsin lamba kan sauran kasashe bisa batun. (Amina)