in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Rasha ya ba da umurnin aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas kan Korea ta arewa
2013-12-03 14:55:57 cri

Wata sanarwa da aka sanya kan shafin yanar gizon mallakar gwamnatin kasar Rasha, ta ruwaito umurnin da shugaban kasar ya bayar a ranar 2 ga wata, inda ya bukaci da a aiwatar da kudurin da kwamitin sulhu na MDD ya zartas a watan Maris, na garkamawa kasar Korea ta arewa takunkumi.

Bisa umurnin da shugaban kasar Vladimir Putin ya bayar, an haramtawa dukkan hukumomi, da kamfanoni, da bankuna, da kungiyoyi ko daidaikun mutane, samarwa Korea ta arewan, ko wane irin taimako ko shawara. Alal misali, an hana samarwa kasar taimakon kera, ko gyara kayayyaki, na'urori, da fasahohin kimiya da sauran ragowar abubuwa, wadanda za su taimaka wajen tabbatar da ci gaban shirin nukiliyar Korea ta arewan. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China