Kwamitin tsaron kasar Korea ta Arewa ya ba da shawara ga Korea ta Kudu a ran Alhamis 16 ga wata, wsdda ta nemi bangarorin biyu su daina shafa ganin laifin juna daga ranar 30 ga wannan wata, sannan a dakatar da ko wani matakin fito na fito tsakaninsu. Haka kuma a dauki matakin da ya dace domin kaucewar barkewar rikicin game da batun nukiliya. Korea ta Arewan na mai bayani game da atisayen soja da Korea ta Kudu ta sanar da cewa, za ta yi tare da Amurka tamkar matakin takala ne, kuma ta nemi wadannan kasashen biyu da su soke aikin.
Ita ma majalisar gudanarwa ta kasar Amurka dangane da wannan sanarwar da Korea ta Arewa, ta bayyana cewa, ya kamata, Korea ta Arewa ta dauki nauyin dake wuyanta na kasa da kasa, da bin yarjejeniyar da bangarori shida suka daddale a shekarar 2005.
Kakakin majalisar madam Jen Psaki ta bayyana a ran 16 ga wata cewa, babbar manufa mai tushe da Amurka ta dauka kan Korea ta Arewa ba ta canja ba, a cikin wata haddadiyar yarjejeniyar da aka daddale a ran 19 ga watan Satumba na shekarar 2005 a cikin shawarwari tsakanin bangarorin shida game da batun nukiliya, Korea ta Arewa ta yi alkawari cewa, za ta yi watsi da dukkan shirye-shirye dangane da makaman nukiliya, da kuma sake bin yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya, har ma da aikin ta karkashin sa idon da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa (IAEA). Amurka kuma ta tabbatar da cewa, ba ta girke makaman nukiliya a zirin Korea ba, hakan ya nuna cewa, ba ta da shirin kai hari kan Korea ta Arewa ta yin amfani da makaman nukiliya ko sauran makamai ba.
Game da sanarwar da Korea ta Arewa ta bayar na cewa, atisayen sojan da Korea ta Kudu da Amurka za su yi tare wani matakin takala ne, kakakin ma'aikatar harkokin waje na kasar Sin Hong Lei ya yi kira a wannan rana ta Alhamis 16 ga wata, ga bangarorin daban-daban da wannan abin ya shafa da su yi hakuri, su kuma guji abin da zai zama takalar fada domin kiyaye zaman lafiya da karko a zirin a halin yanzu. Ma'aikatar tsaron kasar Korea ta Kudu kuwa ta ce, irin wannan atisayen soja na kare kai, ana yin shi a ko wace shekara kuma kasar za ta ci gaba da yin sa. (Amina)