in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta sake tura 'yan sanda masu kwantar da tarzoma zuwa kasar Liberia
2014-07-01 20:51:13 cri
Yau 1 ga watan Yuli da yamma, wani rukunin dake kunshe da 'yan sanda 140 masu kwantar da tarzoma na kasar Sin ya tashi daga nan birnin Beijing zuwa kasar Liberia domin aikin wanzar da zaman lafiya na tsawon watanni 8. Wannan shi ne karo na biyu da kasar Sin ta tura 'yan sanda masu kwantar da tarzoma zuwa kasar Liberia tun watan Oktoba na shekarar bara.

An bayyana cewa, bayan shekara ta 2000, ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ta riga ta tura 'yan sanda fiye da dubu 2 zuwa yankunan da ake shimfida zaman lafiya da M.D.D. ta tabbatar a duk fadin duniya. Ya zuwa yanzu, akwai 'yan sanda 177 da suke aikin wanzar da zaman lafiya a hedkwatar M.D.D. da kasashen Liberia da Sudan ta kudu. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China