in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministar shari'a ta kasar Liberia ta sauka daga mukaminta
2014-10-07 16:04:33 cri
Ministar sharai'a ta kasar Liberia Christina Tah ta mika takardarta ta yin murabus bayan da ta shafe shekaru 6 tana aiki da gwamnatin shugaba Ellen Johnson.

Madam Tah ta bayyana hakan ne a taron manema labarai a Monrovia babban birnin kasar a ranar Litinin, inda ta yi amfani da wannan dama wajen godewa shugaba Sirleaf bisa ga damar da ta ba ta domin ta bauta wa kasarta a matsayin ministar shari'ar na tsawon shekaru 6.

Bugu da kari madam Tah ta godewa al'ummar kasar ta Liberia bisa goyon baya da hadin kan da suka nuna mata a tsawon wadannan shekaru.

Tah ta maye gurbin tsohon ministan shari'ar kasar Francis Johnson Allinson wanda ya kasance ministan shari'ar kasar na farko karkashin gwamnatin Sirleaf kana yanzu yake shugabantar hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasar. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China