Madam Johnson-Sirleaf ta kara da cewa, kasarta ta Liberia da kasar Sin sun yi hadin gwiwa a fannoni daban daban. Masana'antun kasar Sin suna zuba jari a harkokin raya albarkatun ma'adinai a Liberia, kana suna gina hanyoyin mota a kasar, inda lamarin ya samar da kyakkyawan sakamako.
Har wa yau shugabar ta ce, kasarta ta gode wa kasar Sin sosai bisa goyon bayan da take nuna mata. Yanzu kasashen 2 suna kara raya huldar da ke tsakaninsu yadda ya kamata.
Ban da haka, madam Johnson-Sirleaf ta jaddada cewa, a kokarin samar da kyakkyawan yanayi a fuskar raya tattalin arziki da zuba jari, gwamnatin Liberia tana kokarin kyautata tsarin dokokinta, da kuma kara bunkasa ayyukan amfanin jama'a, kamar hanyoyin mota, samar da wutar lantarki da dai sauransu. (Tasallah)