Wannan dai hukunci ya biyo bayan zargin da aka yi wa tsohon shugaban kasar na yin musayar makamai da lu'u-lu'u, tsakaninsa da dakarun da ke adawa da gwamnatin kasar Saliyo, wadanda suka yi amfani da makaman wajen kisan fararen hula kimanin dubu 100, a yakin basasar kasar tsakanin shekarar 1991 zuwa shekarar 2002.
Baya ga wannan an kuma zargi Taylor da aikata wasu karin laifuka, da suka sabbaba yanke masa hukunci cikin watan Afrilun bara, hukuncin da tsohon shugaban Liberian ya kalubalanta a gaban wata kotu ta daban, inda daga bisani kotun daukaka kara ta bukaci a kara masa wa'adin daurin zuwa shekaru 80.
Charles Taylor dake da shekaru 65 da haihuwa ya zama shugaban kasar Liberiya a shekarar 1997, a kuma shekarar 2003, aka hambarar da gwamnatinsa, matakin da ya sanya shi yin gudun hijira zuwa Nijeriya, daga bisani kuma, a watan Maris na shekarar 2006, aka cafke shi a Nijeriyar, ya kuma fuskanci tuhuma a gaban kotu.(Bako)