in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya yi kira da a warware babbar matsalar yankin Sahel
2014-12-12 14:08:26 cri
Zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Liu Jieyi, ya bayyana cewa, ana fuskantar babbar matsalar tsaro, da kuma yaduwar ta'addanci a yankin Sahel dake nahiyar Afirka, don haka ya kamata a mai da hankali matuka ga daukar matakan warware wannan matsala cikin hanzari.

Mr. Liu wanda ya bayyana hakan yayin zaman kwamitin sulhu na MDD na jiya Alhamis, wanda aka gudanar domin tattauna halin da ake ciki a yankin na Sahel, ya kuma bayyana alamu dake nuna ci gaba da habakar zaman karko, da bunkasuwar tattalin arziki da yankin ke samu, yayin da a sa'i daya ake fama da babban kalubalen kiyaye yanayin tsaro, da rashin daidaiton bunkasuwa. Baya ga ayyukan ta'addanci dake ci gaba da yaduwa a yankin, lamarin da ya sa ake samun karin aukuwar laifuffukan da kungiyoyin ta'adda na kasa da kasa ke aikatawa.

Ya ce, kasar Sin na ganin cewa kamata ya yi, a warware matsalar yankin bisa kokarin kasashen da abin ya shafa, da shiyyoyi, da kuma gamayyar kasa da kasa. Kana, ya dace gamayyar kasashen duniya su girmama ikon mallakar kasashen da wannan matsala ta shafa, su kuma taimaka musu wajen ciyar da yunkurin siyasarsu gaba.

Sauran matakan sun hada da kyautata yanayin tsaro, da kuma bunkasa hanyoyin sulhu tsakanin kabilu daban daban, ta yadda za a iya warware manyan matsalolin yankin tun daga tushe. Kaza lika akwai bukatar goyawa yankunan da abin ya fi shafa baya bisa kokarinsu na kiyaye zaman lafiya da lumana a yankin.

Bugu da kari, Mr. Liu ya kara da cewa, gwamantin kasar Sin na mai da hankali sosai kan dangantakar dake tsakaninta da kasashen Afirka, tana kuma fatan taimakawa kasashen dake yankin na Sahel, da yankunan da wannan matsala ta fi shafa yadda ya kamata. Haka kuma, kasar Sin tana goyi bayan MDD dangane da matakan kiyaye zaman lafiya da ta dauka a kasar Mali, kuma tana kokarin tattaunawa tare da kungiyar tarayyar kasashen Afirka ta AU kan harkokin sojoji masu kulawa da matsalolin gaggawa.

Haka kuma, kasar Sin tana da burin yin hadin gwiwa tare da gamayyar kasa da kasa, domin warware matsalolin da yankin Sahel ke fama da su, ta yadda za ta iya ba da gudumawa ga kasashen yankin wajen samun dauwamammen zaman lafiya da lumana. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China